522
Gwamnatin jihar Kano ta ware Naira biliyan 14 domin gudanar da ayyukan raya ƙasa
Kwamishinan Ma’aikatar Yaɗa Labarai, Ibrahim Waiya, ne ya bayyana hakan bayan zaman majalisar zartaswar jihar.
yayin hira da manema labarai a ranar Juma’a a Kano.
Waiya ya ce an ware Naira miliyan 364 domin gyaran asibitin haihuwa na Sabo Bakin Zuwo da ke unguwar Jakara.
Sai Naira miliyan 294 domin gyaran manyan gine-ginen da ake da su a Makarantar Koyar da Fasahar Lafiya ta Bebeji.
An Kuma ware Naira miliyan 113 domin samar da na’urorin hasken rana a asibitoci guda biyar na haihuwa a fadin jihar.
“Za mu kashe sama da Naira miliyan 112 domin samar da magunguna da kayan amfani a asibitocin Hasiya Bayero, Murtala Muhammad, da Yadakunya,” in ji shi.
Ya ce an kuma ware Naira miliyan 272 domin gyara da sabunta wani gida da aka saya a unguwar Zango domin amfanin Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad.