Hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta za ta duba yiyuwar bai wa fursunonin kasar damar kada kuri’a a zaben 2027 mai zuwa.
Shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a yayin da ya karbi bakuncin shugaban hukumar kula da gidajen yari na kasar, Sylvester Nwakuche a ofishinsa kuma wanda ya bukaci yin haka domin acewarsa su ma suna da ‘yanci.